
Sabon shugaban jam’iyyar APC, Nentawe Yilwatda, ya ɗau alwashin ɗaukar matakai don ganin ya ƙara janyo gwamnonin babbar jam’iyyar adawa ta PDP zuwa cikin jam’iyyar mai mulki.
Yilwatda ya bayyana haka ne yayin tattaunawa a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, jim kaɗan bayan zama shugaban APC.
Ya ce baya ga ƴan jam’iyyar PDP da zai janyo zuwa APC, har da wasu ƴaƴan jam’iyyun adawa.
“Abun da na fi mayar da hankali a yanzu shi ne ganin haɗin kan jam’iyyar mu,” in ji shi – inda ya ce zai tabbatar da cewa jam’iyyar ta yaɗa manufofinta yadda ya kamata.
Sabon shugaban jam’iyyar ta APC ya ce duba da irin tarihi da yake da shi a fannoni daban-daban, yana da ƙwarewar da ta kamata wajen jagorantar jam’iyyar mai mulki.