Shugaban rundunar sojojin Najariya, CDS Christopher Musa ya bayyana cewa maganar a rika cewa suna kashe farar hila ta hanyar jefa musu bama-bamai yaudara ce da dabara dan a nuna cewa basu san abinda suke ba.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV inda yace kamin su kai kowane hari, sai sun tabbatar da cewa akwai ‘yan Bindiga a wajan, yace suna da shaidun bidiyo.
Yace ba zasu ce ba’a rasa tsautsai na kashe farar hula ba, yace yawancin hakan na faruwane bayan sun kai hari kan maboyar makaman ‘yan Bindigar.
Yace shin ma wai me yasa sai idan sun fara samun nasara akan ‘yan Bindiga ne sai a rika cewa suna kashe farar hula, kuma me yasa idan ance sun kashe farar hula, kamin su je wajan sai ace an binnesu, ba za’a bari su gudanar da bincike ba?
Yayi zargin cewa kawai ana son kashe musu kwarin gwiwa ne a aikin da suke na yaki da ‘yan ta’adda.