Wednesday, January 15
Shadow

Sakon fatan nasara ga masoyi

Masoyina ina maka fatan Allah ya kareka.

Addu’a nake maka kullun Rabbana ya hore.

Allah yasa ka fi haka.

Masoyina Allah ya kawo budin kasuwa ya daukaka ka akan sa’anninka.

Ina maka fatan kamar yanda kake neman Arziki ta hanyar halaliya, Allah ya Azurtaka ta hanyar halaliya.

Ina Addu’ar Allah ya makantar da kai daga ganin haram, ya bude idanunka wajan ganin halal, Allah ya hana bakinka cin haram, ya bude maka shi wajan cin halal, Allah ya daure hannuwanka kada su kai ga Haram, Ya sakesu su yi walwala wajan yakin neman Halal.

Masoyina kullun ina alfahari da kai kan yanda kake jajircewa wajan neman na kanka, ina fatan Allah ya wadatar dakai.

Karanta Wannan  Nasiha ga masoyiyata

Makiyanka sai sun yi kunci saboda nasarar da zaka samu, mahassadanka sai ciwon zuciya ya kamasu saboda daukakar da zaka samu, sa’anninka sai sun yi mamakin arzikin da zaka samu da yardar Allah.

Ina fatan Allah ya daukaka ka akan sana’arka yasa itace silar arziki.

Masoyina ina maka fatan wuce Dangote wajan arziki, Amin.

Jarabawa na zuwa ta kowane fanni, ina fatan Allah kada ya dora maka jarabawar da ba zaka iya dauka ba, yasa kada hankalinka ya gushe daga cin halal.

‘Ya’yan mu zasu yi rayuwa me kyau da tsafta saboda mahaifinsu jajirtaccene, Allah ya karo nasara masoyina.

Na daukeka a matsayin jagorana saboda kai jajirtaccene wajan nema, wajan magana, wajan iya kwalliya, wajan karfin zuciya, Nasara na tare da kai.

Karanta Wannan  Addu'ar barka da safiya

Masoyina Allah ya kara maka karfin zuciya dana jiki dana nema dana hawa dokin Nasara wanda ba tuntube bare faduwa Insha Allahu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *