Sunday, March 16
Shadow

Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na wata karo bakwai a tarihi

Ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan gasar Premier na wata-wata karo na bakwai a tarihin.

Mohamed Salah ya lashe kyautar watan Fabrairu a matsayin ɗan wasan da ya fi hazaƙa a watan, bayan da bajintar da ya yi a watan, a ƙoƙarin da ƙungiyarsa ke yi na lashe gasar Premier.

Ɗan wasan na ƙasar Masar ya ci ƙwallo shida, ciki har da biyu da ya zura a ragar Bournmouth da wanda ya zura a ragar Manchester City a watan, sannan ya taimaka aka ci huɗu.

Mo Salah ya samu kyautar ne bayan doke Beto da Jean-Philippe Mateta da Yankuba da Djed Spence da kuma Dominik Szoboszlai.

Karanta Wannan  Babu Gaskiya Game Da Jita-Jiťàŕ Da Ake Yadawa Cewa Jirage Na Kawowa 'Ýan Bìnđìģa Maķàmài Su Kuma Kwashi Ģwàĺ A Zàmfàra

Da wannan nasara, a yanzu Salah ya kamo tarihin da Sergio Aguero da Harry Kane suka kafa na cin kyautar sau bakwai.

Sannan ya zarta Steven Gerrard da Cristiano Ronaldo waɗanda suka ci kyautar sau shida.

Salah ya samu kyautar ce a watannin Nuwamban 2017 da Fabrairun 2018, da Maris ɗin 2021 da Oktoban 2021 da Oktoban 2023 da Nuwamban 2024 sai kuma Fabrairun 2025.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *