
Kakakin majalisar Dattijai Sanata Godswill Akpabio ya gargadi Kingsley Udeh (SAN) da cewa, kada ya sake ya amsa tambaya akan shugaban kasar Amirkaz Donald Trump.
Ya bayyana masa hakane ranar Alhamis yayin tantance shi dan bashi ministan kimiyya da Fasaha.
Bayan da Kingsley Udeh (SAN) ya gabatar da kansa a gaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya bayar da damar a masa tambayoyi amma ya gargadeshi da cewa, kada ya amsa tambaya akan shugaban kasar Amirka, Donald Trump.
A karshe dai majalisar ta amince da nadin Kingsley a matsayin Ministan.
Shidai Godswill Akpabio a baya yace bai isa ya baiwa Trump amsa ba sai abinda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yace.
trump dai na barazanar kawo Khari Najeriya.