
Sanata Lado ya miƙa kyaututtukan gidaje ga waɗanda su ka yi na ɗaya da na biyu a musabaƙar Kur’ani a Kano
Sanata Bashir Lado ya miƙa kyaututtukan gidaje ga waɗanda su ka yi na ɗaya da na biyu a musabaƙar Kur’ani da aka kammala kwanannan a jihar Kano.
Kyaututtukan sun haɗa da gidaje biyu masu dakuna biyu da falo ga wadanda suka yi na biyu a gasar , da kuma gidaje masu dakuna uku ga wadanda suka yi na ɗaya a musabaƙar.
Wadanda suka samu nasarar sun hada da:
Maryam Abubakar Mu’az (wacce ta zo ta ɗaya a izifi 60 a mata, Ahmad Shu’aib (wanda ya yi ma daya a izifi 60 a maza), Zainab Hassan Shu’aib (ta biyu a izifi 60 a mata), da Ahmad Kabir Baturi (na biyu a izifi 60 a maza).
Da ya ke jawabi jim kadan bayan mika mukullayen gidajen, Sen.Lado, wanda ya shirya gasar, ya ce an gudanar da musabaƙar ne domin tunawa da karrama marigayiya Alhaja Abibatu Mogaji Tinubu, mahaifiyar shugaban kasa Bola Tinubu.
Lado wanda ya samu wakilcin Farfesa Ali Muhammad, mataimakin shugaban kwamitin shirya gasar ya ce an kuma shirya gasar ne domin cusa kyawawan dabi’u na Alkur’ani mai girma a zukatan matasan Musulmin Najeriya.