Friday, October 9
Shadow

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jinjinawa Hilda Baci wadda ta dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jinjinawa Hilda Baci wadda ta dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya.

Shugaban kasar yayi wannan jinjinane ta bakin ministan yada labarai, Mohammed Idris, inda yace abinda Hilda ta yi ya jawowa Najeriya suna a Idon Duniya kuma yace ‘yan kasa na al’fahari da ita.

Shugaban yace, matasa su yi koyi da irin abinda Hilda ta yi inda ya sha alwashin cewa gwamnati zata tallafawa irin wannan kokari nan gaba.

Hilda Baci dai ta yi wannan abu ne dan shiga kundin Tarihin Duniya hakanan a shekarar 2023 ma ta yi girki na lokaci mafi tsawo a Duniya.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Shugaban NNPLC ya koma bakin aiki yayin da ake rade-radin an koreshi saboda zargin yana munafurtar shugaban kasa yana taimakawa 'yan Adawa watau su Atiku Abubakar, saidai wata majiya tace Matar shugaban kasa, Remi Tinubu ce ta hana a koreshi daga aiki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *