
A ranar Talata me zuwa ne ake sa ran Sanata Natasha Akpoti zata gurfana a gaban kotu.
Rahotanni sun bayyana cewa, Lauyan Sanata Natasha, West Idahosa (SAN) ne ya bayar da tabbacin.
Yace a matsayin sanata Natasha na ‘yar kasa ta gari me bin doka, zata bayyana a gaban kotun kamar yanda aka bukata.
Gwamnatin Tarayya ta shigar da karar Sanata Natasha Akpoti ne ta hannun wailinta, Mohammed Abubakar inda take zargin Natasha da bata suna.
Gwamnatin ta yi zargin Sanata Natasha Akpoti tace wai kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello sun yi yunkurin kasheta.
Sannan tace wai Sanata Godswill Akpabio yana safarar sassan jikin dan adam kamar yanda ta gayawa wata mata.
Daga cikin shaidun da gwamnatin tarayya zata gabatar a wannan karar, Akwai Sanata Godswill Akpabio da Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello da wasu mutane 4.