
Sanatan Amurka, Ted Cruz wanda shine ya kai kudirin dokar da ta saka Najeriya cikin jerin kasashen da Amurkar ke sakawa ido bisa zargin anawa Kiristoci khisan Kyiyashi a yanzu kuma ya sake kai wani Kudirin dokar majalisar kasar.
Ted Cruz ya godewa shugaban kasa, Donald Trump kan matakin da ya dauka akan Najeriya inda yace a baya lokacin mulkin Trump na farko, ya saka Najeriya cikin kasashen da Amurka zata rika sakawa ido amma tsohon shugaban kasar, Biden ya cireta.
Saidai yace ya ji dadi da a yanzu Trump ya dawo da Najeriya cikin kasashen da Amurka zata rika sakawa ido.
Yace a yanzu ya sake gabatar da wata sabuwar kudirin doka da zata hukunta wasu ‘yan Najeriya da ake zargi da hannu wajan Muzgunawa Kiristoci sannan ya ce zakuma a dauki hukunci kan jihohi 12 na Arewa dake amfani da shari’ar Musulunci.
Hakanan yace zasu tabbatar an daina hukunta masu yin batanci ga addinin Musulunci.