
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, Sanata Ted Cruz wanda shine kan gaba wajan zuga shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kawowa Najeriya hari zai tsaya takarar shugaban kasar a zaben shekarar 2028 me zuwa.
Ko da a zaben fitar da gwani na jam’iyyar Republican na shekarar 2016 Sanata Ted Cruz ya taba tsayawa takarar shugaban kasa inda ya zo na biyu, Trump ya kayar dashi.
Wannan bayyana aniyar tasa ta fito da mabanbanta ra’ayoyi inda wasu amurkawa ke cewa zasu zabeshi wasu kuma na cewa ba zasu zabeshi ba.