
Sanata Godswill Akpabio ya gayawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu cewa sanatoci sun ce ya rokeshi ya sake duba janye musu jami’an tsaron da yayi.
Sanata Akpabio ya gayawa shugaba Tinubu hakanne a yayin da shugaban ya je gabatar da kasafin kudin shekarar 2026a zauren majalisar.
A baya dai shugaba Tinubu ya bayar da umarnin janyewa duk wani babba a kasarnan jami’an tsaron ‘yansanda.