Monday, December 16
Shadow

Sarkin Musulmi Ya Karrama Matashi Mai Aikin Shara Da Ya Tsinci Kimanin Naira Milyan 16 Ya Maida A Filin Jirgin Sama Na Kano

Daga Mukhtar A. Haliru Tambuwal Sokoto

Matashin nan mai aikin shara a filin jirgin sama na kasa da kasa dake Kano, Auwal Ahmad Dankode da ya tsinci makudan kudi ya maida a kwanan baya (dalar Amurka dubu goma a wancan lokacin kimanin naira miliyan 16) ya kasance cikin wadanda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alh. Muhammad Saad Abubakar CFR mni ya karrama a lokacin rufe taron makon Danfodiyo karo na 11 da aka gabatar a Sokoto.

A duk shekara Mai Alfarma Sarkin Musulmi na karrama zababbun mutane da kuma wadanda suka yi wata bajinta ta hidima ga al’umma, ko addini ko makamantansa.

An karrama wanda ya tsinci kudi cikin Keke Napep da wadda ta cinci kudi a Aikin Hajji, duk da matsin halin da ake ciki.

Karanta Wannan  KISHI KUMALLON MATA: Uwargida Ta Shiga Gaban Mijinta A Yayin Da Yake Daukar Hoto Da Sabuwar Amaryarsa

‘Ýan Nijeriya sun yi suna wajen tsinta da maida abin da suka tsinta ciki da wajen wannan kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *