
Wani Bidiyo ya bayyana a kafafen sada zumunta dake nuna wani da aka bayyana a matsayin daya daga cikin ‘yan Bindigar da suka sace daliban makaranta.
A cikin Bidiyon an jishi yana cewa, ai an san inda suke a zo a kubutar da daliban idan an isa.
Lamarin ya dagawa mutane hankula inda da yawa ke cewa lallai akwai matsala idan har dan Bindiga zai iya fitowa yana wannan kalami.