
Shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu dake daure ake zarginsa da cin amanar kasa ya sha Alwashin ba zai kara zuwa kotu ba.
Kanu ya bayyana hakane inda yace shari’ar da ake masa yaudara ce kawai.
Kanu yace dalili daya zai sashi ya ci gaba da zuwa kotu shine idan za’a gurfanar dashi a gaban kotun dake da cikkakken ikon a kudin tsarin mulkin Najeriya.
Kanu ya kawo dalilai da yawa da yace yana ga kotunan da ake kaishi a yanzu ba zasu iya masa hukuncin da ya dace ba.