
Wasu rahotanni daga majiyoyi daban-daban dake ta yawo shine Tsohon Gwamnan Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso zai koma APC.
Saidai maganar tana ta jan kafa.
A wata majiya, munji cewa sharudan da ake neman gindayawa ne yasa maganar ke jan kafa inda ake ci gaba da tattaunawa me zafi.
Daya daga cikin sharudan shine za’a baiwa tsohon gwamnan Kanon mukamin mataimakin shugaban kasa a 2027.
Saidai idan hakan ta faru, shi Kuma Ganduje shine zai kawo wanda zai zama Gwamnan Kano a 2027.
Yayin da shi kuma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf bayan kammala wa’adin mulkinsa na farko, za’a bashi mukamin zama cikin kwamitin gudanarwa na jami’ar Yusuf Maitama Sule.
Saidai duka wadannan bayanai ba’a hukumance aka sakesu ba, wata majiya ce ta bayyanasu.