
Kungiyar Kwadago ta kasa, NLC ta gayawa kungiyar bada Lamuni ta Duniya IMF cewa shawarwarin gyara da suke baiwa shuwagabannin Najeriya na jefa mutane cikin halin kaka nikayi.
NLC ta gayawa IMF hakane a yayin da wakilan IMF din suka zo Najeriya suka je ofishin NLC dan su ji yanda ake ciki game da irin abinda ‘yan Najeriya ke cewa kan tsare-tsaren gwamnati.
Wakilan IMF biyu, Christian H. Ebeke da Axel Schimmelpfennig ne suka wakilci kungiyar zuwa ofishin NLC.
Sun bayyana cewa, IMF tana bayar da shawara ne kawai, bata tursasa kasashe amfani da shawarwarin da take basu.
Sannan sun ce mafi yawanci kasashe basa aiwatar da shawarwarin IMF din yanda ya kamata.
A nasa bangaren shugaban NLC Joe Ajaero ya bayyana cewa tsare-tsare irin su cire tallafin mai wanda dama can babu shi kawai an yi amfani dashi ne dan kara farashin man fetur sun jefa mutane cikin talauci da yunwa.
Yace abin takaici ma shine ina aka kai kudin tallafin man fetur din da aka ce an cire?