
Babban malamin addinin islama, Sheikh Sani Rijiyar Lemu yayi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sauke shugaban hukumar zabe me zaman kanta.
Yace shugaban hukumar zaben kasancewarsa mutum dake da fenti na nuna kiyayya ga Musulmai, ba’a tunanin zai yi adalci a zabe.
Yace kuma Adalci shine idan aka nadawa mutane shugaba suka ce basa sonshi, a saukeshi saboda samun Maslaha.