SHEKARA 16 DA AURE BATARE DA YAJI BA BALLE SAKI.
Darakta a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood Hassan Giggs sun cika shekara 16 da aure shi da matarsa, Jarumar Kannywood Muhibbat Abdussalam tare da samun ƙaruwar arziƙin ƴaƴa mata 3 kamar yadda kuke gani cikin wannan hoto.
Sun rayu tsawon waɗannan shekaru batare da yaji ba balle saki. Wannan gagarumin abin alfahari ne a masana’antar Kannywood.
Muna musu fatan alkhairi Allah Ya ƙara musu aminci da zaman lafiya cikin so da ƙaunar juna mai ɗorewa.
Wane fata zaku yi musu?