Friday, December 5
Shadow

Shekaru 2 sun yi kadan ace za’a duba a ga na yi kokari ko ban yi ba, Kamata yayi sai nan da shekaru 10 zuwa 12 kamin ace za’a min hukunci kan mulkin Najeriya>>Tinubu

A yayin da ya cika shekaru 2 da mulki, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, shekaru 2 sun yi kadan ace za’a duba a ga yayi kokari ko bai yi kokari ba.

Yace yawanci masana sun ce sai an shekara 10 zuwa 12 idan aka samu canji sannan a duba a ga ko an samu ci gaba ko ba’a samu ba.

Ya bayyana hakanne ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga.

Shugaban yace nan ba da jimawa ba ‘yan Najeriya zasu ga alfanun matakan gyara tattalin arziki da ya dauka.

Karanta Wannan  Kudin Dangote sun karu zuwa Dala Biliyan $30.2

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *