
Rahotanni sun bayyana cewa, Kasa Saudiyya ta dakatar da bayar da Bizar aiki ga ‘yan Najeriya da sauran kasashe masu yawa.
Kasashen da wannan lamari ya shafa sun hada da Indonesia, Iraq, Jordan, Yemen, India, Pakistan da Bangladesh.
Sauran sune Egypt, Algeria, Sudan, Ethiopia, Tunisia da Morocco.
Rahoton yace, Ma’aikatar kula da ci gaba al’umma da kasar Saudiyyar ne ta sanar da hakan.
Kuma an dauki wannan mataki ne dan baiwa mahajjata damar gudanar da aikin Hajji, idan aka kammala aikin Hajji nan da karshen watan Yuni za’a ci gaba da bayar da bizar.