
Dr. Ifeanyi Okowa, mataimakin Atiku a takarar shugabancin ƙasa a zaben 2023 ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Okowa ya koma APC din ne tare da Sheriff Oborevwori, gwamnan jihar Delta Kuma magajin sa.
Hakazalika gaba ɗaya shugabancin PDP na jihar ta Delta ya narke cikin APC, kamar yadda sanarwa ta gabata a yau Laraba.