Eh, shigar ciki nasa ciwon mara, mata da yawa na yin fama da ciwon mara bayan sun dauki ciki.
Kuma zai iya zuwa a kowane lokaci, watau a farkon shigar ciki ko kuma yayin da cikin ya tsufa.
Wata zai rika zuwa mata yana tafiya lokaci zuwa lokaci, zata rika jinshi kamar irin na al’ada.
Za’a iya jinshi a gefe daya na mara inda a wasu lokutan za’a iya jinshi a duka bangarorin biyu na marar.
Wannan ciwon mara ba wata babbar matsala bace, an saba ganinta a wajan mata masu ciki da yawa. Zafin ciwon kan iya karuwa yayin da cikin ke kara girma.
Saidai idan an shiga damuwa sosai saboda ciwon na mara ana iya zuwa ganin Likita.