Wednesday, January 15
Shadow

Shin Allah yana yafe laifin zina?

Da Sunan Alah mai rahama mai jinkai, dukan yabo da girmamawa sun tabbata ga Allah ubangijin talikai.

Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad(SAW) Manzonsa ne.

Shin ka taba yin Zina, kana da niyyar yi bisa sanin cewa haramun ce amma ka tuba daga baya?

Shin Allah yana yafe laifin Zina idan aka tuba?

Zina na daya daga cikin manyan laifuka a addinin musulunci.

Allah madaukakin sarki ya fada mana a Qur’ani cewa,’ Kada ku kusanci Zina, Alfashace kuma hanya ce ta shedan’ Qur’an 17:32.

Hakanan kuma Allah madaukakin sarki na cewa

‘Kuma Wadannan da basu hada Allah da wani ba wajan bauta, basu kashe ran da Allah ya hana a kashe ba, saidai bisa gaskiya, kuma basu aikata Zina ba. Amma duk wanda ya aikata haka, zai gamu da Azaba. Zai gamu da Azaba nunki ba nunki a ranar tashin qiyama kuma zai dawwama akanta yana kaskantacce. Sai fa Wanda suka tuba, suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka na kwarai. Wadannan Allah zai maye munanan ayyukansu da kyawawa, Allah mai yawan Gafara da kuma jin kai ne’ Qur’an 25: 68-70.

Karanta Wannan  Maganin daina zina

Girman zunubi na karuwane yayin da mutum ya dawwama yana aikatashi.

Dan haka musulmi na gari ya kamata ya ji tsoron Allah ya daina aikata wannan mummunan Zunubi na Zina. Mutum ya rika tunawa da fushin Allah da kuma Azabarsa a ranar tashin qiyama.

Sannan kuma mutum ya rika tuna irin kaskancin da zai gamu dashi a Duniya dalilin Zina idan Asirinsa ya tonu, ya kuma rika tuna irin shaidar da mutane zasu rika bayarwa akansa idan ya mutu. Ya kuma rika tuna irin cututtukan da zasu iya samunsa dalilin zina, irin su cutar Kanjamau, cutar sanyi da sauransu.

Mutum ya daina nacewa akan aikata Zunubi da tunanin cewa, Allah zai yafe masa dan kuwa baisan cewa ko Allah zai karbi tuban nasa ba.

Karanta Wannan  Maganin daina zina

Hakanan dagewa akan aikata Zunubi yana nisantar da mutum daga Allah wanda hakan ke sa zuciya bushewa, har mutum ya shagala, ya manta da tuba, idan ba’a yi sa’a ba, mutum na iya mutuwa yana aikata wannan zunubi.

Dan haka musulmi ya guji dukkan zunubi, babba ko karami. Amma idan mutum ya aikata laifi, ya gaggauta tuba, tuba na gaskiya, da niyyar cewa ba zai kuma aikata wannan Zunubiba, kuma yayi nadama, a ji zafin abinda ya aikata a zuciyarsa. Allah yana karbar tuba, tuba ta gaskiya.

Zina bijirewa Allah ne sannan kuma cin zarafin wanda aka aikata Zinar da itane, ko dashine.

Karanta Wannan  Maganin daina zina

Kima da mutuncin Mutane na da matukar muhimmanci a musulunci, Mutum ya kuma nemi yafiyar wanda ya munanawa ko kuma yaci zarafinsa kamin ya mutu, idan ba haka ba, za’a biyasu da ladarsa, ko kuma a dauki zunubinsu a dorasa masa.

Allah ne masani.

Idan akwai kuskure, daga garenine, kuma idan akwai wanda ya lura da kuskuren, ya min gyara a kasan comment.

Da fatan wannan bayani ya gamsar game da tambayar Allah yana yafewa mazinaci?Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *