
Rahotanni na ta yawo a kafafen sada zumunta cewa, wai an kai Khari gidan babban malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi.
Wasu Rahotannin na cewa, wai Bom ne aka jefawa gidan malamin.
Saidai Masallacin Sultan Bello inda nan ne malam ke karatu, ya musanta wannan rahoton.
Wakilin hutudole da yayi sallah a Masallacin ya ruwaito cewa, malam Nasiru wanda aka fi sani da Dan Agaji, ya ce jiya sun rika samun kiraye-kiraye ana tambayar lafiyar malam da kuma jin cewa ko da gaske an jefawa gidansa Bom?
Yace labarin karyane kuma lafiyar malam Qalau.
Ya bayyana cewa, Masu neman Malam Da sharri ne suka rika yada wannan labarin.