
Rahotanni nata yawo a kafafen sada zumunta cewa babban malamin Addinin Islama, Sheikh Isa Ali Pantami ya koma jam’iyyar ADC daga jam’iyyar APC.
A kwanannan dai ana ta ganin shuwagabannin jam’iyyun siyasa na ta zawarcin Pantami inda suke kai masa ziyara gida.
Lamarin ya dauki hankula inda ake ta muhawara masu zafi.
Saidai har yanzu shi Pantami ko wata kafa me zaman kanta bata fito ta tabbatar da komawarsa jam’iyyar ADC ba.