Wednesday, January 15
Shadow

Shin maniyyi najasa ne

A bisa tsarin addinin Musulunci, maniyyi ba najasa ba ne.

A mazhabar Malikiyya, Shafi’iyya, da Hanbaliyya, maniyyi ana daukarsa da tsarki.

A mazhabar Hanafiyya kuma, maniyyi ana daukarsa mai tsarki amma idan ya taba tufafi, ya kamata a wanke wuri.

Amma, duk da haka, ana bukatar yin wanka (ghusl) bayan saduwa ko fitar maniyyi.

A mazhabar Abu Hanifa da Ahmad idan maniyyi ya taba kaya za’a iya kankareshi kawai ba sai an wanke ba ya wadatar.

Saidai a Mazhabar malikiyya, sun ce dole sai an wankeshi.

Shaykh Al-Islam Ibn Taymiyah yace magana mafi inganci itace Maniyyi ba najasa bane kamar yanda Ash-Shafi`i da Ahmad suka dauka.

Karin Hujja kan cewa Maniyyi ba najasa bane daga Hadisai:

Karanta Wannan  Yadda ake gane maniyyi mace

Matar Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) A’isha R.A ta bayyana cewa ta tuna wasu lokutan takan kankare maniyyi daga tufafin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi wasallam) kuma yakan yi sallah da tufafin.

Sanannen Abune cewa, Najasa ba’a kankareta saidai a wanke.

Hakanan asalin mutane masu daraja a wajen Allah kamar Annabawa, Masu gaskiya, Shahidai, da mutane na gari duk daga wannan ruwane, dan haka asalin irin wadannan mutane mutane ba zai zama najasa ba. (Ash-Sharh Al-Mumti‘, 1/388)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *