
Majalisar Zartaswa a zamanta na ranar Litinin ta amince da fitar da kudade da ayyukan gina tituna a sassa daban-daban na Najeriya.
Bayan kammala zaman, Ministan Ayyuka, Dave Umahi ya bayyanawa manema labarai cewa, akwai sabbin ayyukan titi da wanda ake sabuntawa a jihohi 13.
Yace wasu daga cikin titunan da za’a yi sun hada da na garuruwan Akure-Eta-Ogbese-Iju-Ekiti zuwa garuruwan Ikere-Ado-Ekiti wanda suke tsakanin jihohin Ondo da Ekiti.
Yace akwa kuma Tagwayen titunan da za’a gina a hanyar Sokoto-Zamfara-Katsina-Kaduna.
Sannan kuma akwai titin Maiduguri-Monguno a jihar Borno.
Sauran Titunan da za’a gina sune na Aba-Ikot-Ekpene, da titin Ebute-Ero.
Akwa kuma Tituna Gombe-Yola.
Sannan Akwai Titin Benin-Shagamu-Ore.
Akwai kuma titin Enugu-Onitsha.
Sannan Akwai titin Atan-Alapoti-Ado-Odo a jihar Ogun.