Friday, December 6
Shadow

Sojojin Najeriya sun tabbatar da bullar sabuwar kungiyar ‘yan tà’àddà a kasar

Mai magana da yawun rundunar Manjo Janar Edward Buba ya ce ‘yayan wannan sabuwar kungiyar sun fito ne daga kasashen Nijar da Mali, kuma ya zuwa yanzu ba’a iya sanin manufar kungiyar ba.

Buba yace wannan sabuwar kungiyar wadda ta bullo bayan juyin mulkin da akayi a Nijar, ta haifar da matsala a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a iyakokin Nijar da Najeriya.

Buba yace dakarun kasashen 2 na ci gaba da daukar mataki domin tabbatar da tsaro a kan iyakokon yankin.

Idan baku manta ba, a ranar litinin da ta gabata, RFI Hausa ya gabatar muku da rahoto a kan bullar wannan kungiya daga Sokoto.

Karanta Wannan  Majalisar tarayya ta fara tantance sabbin ministoci

Bullar wannan kungiyar ya dada tabbatar da karuwar matsalar tsaron da ake fuskanta a yankin arewa maso yammacin Najeriya da rikicin ‘yan bindiga ya daidaita wajen hallaka jama’a da kuma raba dubban mutane da garuruwansu, abinda ya kai ga wasu samun mafaka a Jamhuriyar Nijar.

Kakakin sojin ya ce a watan da ya gabata, dakarun Najeriya sun hallaka ‘yan ta’adda 163 tare da kama wasu 82 da kuma kubutar da akalla mutane 80 da akayi garkuwa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *