
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shan suka saboda wallafa hoton da ake zargin an yishi da AI(watau hoton Boge)
Shugaban ya wallafa hotonne ta shafinsa na X.
Ya wallafa cewa yana tare da shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame inda aka gansu tare zaune.
Saidai an gano cewa hoton da AI aka yishi.
Hakan ya jawowa shugaban kasar suka sosai inda da yawa suka ce hakan abin kunyane ga Najeriya.