Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa sabuwar dokar canja fasalin biyan manyan sojoji da suka ajiye aiki hakkokinsu.
A sabuwar dokar, Soja da ya aije aiki yana da mukamin CDS, za’a rika bashi Dala dubu $20 duk shekara na kula da lafiyarsa a kasar waje, sannan za’a bashi mota jif wadda harsashi baya hudata, kuma hukumar soji ce zata rika kula da motar sannan bayan duk shekara hudu za’a rika canja mai motar.
Sannan za’a bashi mota Peugeot 504 ko wata kwatankwacinta sannan kuma za’a bashi ma’aikata 5, da suka hada da masu dafa abinci 2, me ban ruwan fulawa, da wasu karin masu hidima biyu.
Zakuma a bashi me gadi mutum daya da Mataimaki na musamman guda daya, sai direbobi 3, sannan kuma duk sanda yake bukatar karin jami’an tsaro, za’a bashi.
Sannan kuma zai ci gaba da rike bindigarsa.
Shi kuma soja wanda yayi ritaya yana da mukamin Lieutenant generals za’a bashi motoci 2 kirar Toyota Hilux ko Toyota Land Cruiser da dala dubu 20 duk shekara dan zuwa ganin likita a kasar waje, masu dafa abinci 2, da karin wasu ma’aikata 2, sojoji 4 da zasu rika gadin gidansa, direbobi 2, da kuma wanda zai rika take masa baya guda daya.
Su kuma wanda suka ajiye aiki a mukamin Major General da Brigadier General za’a basu mota kirar Toyota Land Cruiser da dala dubu $15 duk shekara dan zuwa kasar waje neman magani da ma’aikatan gida da masu gadi.
Shi kima janar me anini daya watau, One star General, Brigadier General za’a rika bashi Dala dubu $10 duk shekara dan zuwa kasar waje neman magani, da mota kirar Toyota Camry, da kuma ma’aikata da masu gadin gida.
Soja da yayi ritaya yana da mukamin Colonel kuma zai samu mota kirar Toyota Corolla da duba lafiyarsa kyauta a Najeriya