Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, Mutanen Kano ba zasu sake goyawa Kwankwaso baya ba.
Yace ko da a 2023 ma rikicin cikin gida na Jam’iyyar APC ne yasa Kwankwaso yayi nasara a zaben, yace amma wanda suka zabi Jam’iyyarsa ta NNPP a yanzu suna nadama.
Ya bayyana hakane a wajan taron karrama jiga-jigan Jam’iyyar da aka yi inda shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya wakilceshi.
Ganduje yace yakan yi mamaki idan yaji Kwankwaso na cewa yana da goyon bayan mutanen jihar, yace gashinan Gwamna Abba Kabir Yusuf ma duk a rude yake bai san abinda ke tafiya a gwamnatinsa ba.
Ganduje yayi kira ga ‘yan Jam’iyyar ta APC da su hada kansu inda yace ta hanyar hakane musamman zasu samu nasarar kwace Jiyar daga hannun NNPP.