
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa jami’an tsaron Najeriya umarnin su gaggauta magance matsalar tsaron Najeriya.
Tinubu ya bayar da wannan umarnine biyo bayan rahotanni dake cewa an kashe mutane kusan 200 a jihar Benue.
A baya dai har shugaban sojojin Najeriya sai da ya sanar da komawa jihar ta Benue da dama saboda kamarin matsalar tsaron jihar.
Cikin wadanda aka kashe a wannan sabon harin hadda jami’an tsaro 5.