Friday, June 26
Shadow

Shugaba Tinubu ya bar Abuja dan ziyara zuwa kasashen Japan da Brazil

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bar Abuja a yau, Juma’a dan zuwa kasashen Japan da Brazil ziyara.

Shugaban zai tsaya a Dubai, UAE kamin ya ci gaba da tafiyar tasa.

Shugaba Tinubu ya tashi daga filin jirgin Nnamdi Azikiwe da misalin karfe 11:15 na safiyar yau.

Manyan jami’an gwamnati da suka hada da shugaban ma’aikatan fadar Gwamnati, Femi Gbajabiamila, da babban me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da Ministan kudi, Wale Edun sun halarci filin jirgin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Ina neman 'Yan Najeriya su taramin Raguna 100 zan yi wani aiki duk Tshàgyèràn Dhàjì sai sun shèkyè>>Inji Wannan dake ikirarin Malumta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *