Wednesday, May 28
Shadow

Shugaba Tinubu ya bar Katsina bayan ziyarar Kwanaki biyu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bar Katsina bayan kammala ziyarar kwanki biyu da ya je jihar.

D misalin karfe 3 na yammacin ranar Asabar ne jirgin shugaban kasar ya bar filin jirgin sama na Umar Musa ‘Yaradua dake jihar.

Shugaba Tinubu a yayjn ziyararsa a jihar Katsina ya ziyarci sojoji inda ya karfafa musu gwiwa sannan ya kaddamar da wasu ayyuka biyu na titi da wata cibiyar ayyukan noma da gwamnatin jihar ta gina.

A yau Asabar kuma shugaba Tinubu ya halarci daurin auren diyar gwamnan jihar Dikko Radda kamin barin Katsina.

Karanta Wannan  Jarumin Finafinan Hausa, Ayatullahi Tage Ya Angonce A Karon Farko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *