Sunday, March 16
Shadow

Shugaba Tinubu ya kaddamar da titin Legas zuwa Ibadan da aka kammala

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kaddamar da titin Legas zuwa Ibadan da aka kammala wani sashe inda ake ci gaba da aiki a wani sashe na titin.

A yayin kaddamarwar, Shugaba Tinubu ya bayyana muhimmancin Titi wajan karfafa tattalin arzikin kasa.

Ya bayyana cewa, Gwamnatinsa zata yi kaimi wajan tabbatar da samar da tituna da zasu hada birane da karkara dan ci gaban tattalin arzikin kasa.

Shugaban kasar wanda gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya wakilta ya bayyana cewa, yana kuma jinjinawa ministan ayyuka, Dave Umahi kan jajircewarsa.

Karanta Wannan  Harin da ya kashe mutum 10 a New Orleans ba na ta'addanci ba ne - FBI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *