Friday, December 5
Shadow

Shugaba Tinubu ya nada dan tsohon shugaba kasa, IBB babban mukami

Tinubu ya naɗa ɗan tsohon shugaban ƙasa, IBB a matsayin shugaban Bankin Noma na Ƙasa.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Muhammad Babangida, ɗan tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), a matsayin Shugaban Bankin Noma na Ƙasa (BOA).

Sanarwar naɗin ta fito ne a ranar Juma’a ta bakin Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin yada labarai .

A cewar Onanuga, shugaban ƙasa ya amince da naɗin ne a yau Juma’a tare da wasu mutane guda bakwai.

“Wasu daga cikinsu za su yi aiki a matsayin shugabanni na hukumomin gwamnatin tarayya,” in ji shi.

A cewar sanarwar, Muhammad Babangida ya yi karatu a Jami’ar Turai da ke Montreux, Switzerland, inda ya samu digiri na farko a fannin Gudanar da Kasuwanci (Business Administration) da kuma digirin digirgir (Master’s) a fannin Hulɗar Jama’a da Sadarwar Kasuwanci.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Anata ta rububin daukar hotuna yayin da wai Gibirima ya bayana a bango a Najeriya yayin Maulidi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *