Tuesday, May 19
Shadow

Shugaba Tinubu ya nada dan tsohon shugaba kasa, IBB babban mukami

Tinubu ya naɗa ɗan tsohon shugaban ƙasa, IBB a matsayin shugaban Bankin Noma na Ƙasa.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Muhammad Babangida, ɗan tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), a matsayin Shugaban Bankin Noma na Ƙasa (BOA).

Sanarwar naɗin ta fito ne a ranar Juma’a ta bakin Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin yada labarai .

A cewar Onanuga, shugaban ƙasa ya amince da naɗin ne a yau Juma’a tare da wasu mutane guda bakwai.

“Wasu daga cikinsu za su yi aiki a matsayin shugabanni na hukumomin gwamnatin tarayya,” in ji shi.

A cewar sanarwar, Muhammad Babangida ya yi karatu a Jami’ar Turai da ke Montreux, Switzerland, inda ya samu digiri na farko a fannin Gudanar da Kasuwanci (Business Administration) da kuma digirin digirgir (Master’s) a fannin Hulɗar Jama’a da Sadarwar Kasuwanci.

Karanta Wannan  Mun Dauki Tsawon Shekaru Talatin Muna Aiki Ba Dare Ba Rana, Amma Yanzu Hakkiñmu Ya Gagara Fita Da Za Mu Ciyar Da Iyalanmu, Cewar Tsoffin 'Yan Sandan Nijeriya Dake Zañgà-Zañgà A Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *