Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Manjo Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Olufemi zai ci gaba da riƙe muƙamin har lokacin da Janar Taoreed Lagbaja zai koma ƙasar.
Kafin naɗa shi a muƙamin, Oluyede ne kwamandan runduna ta 56 da ke Jaji a jihar Kaduna.
Tun a makon da ya gabata rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa Janar Lagbaja yana jinya a wani asibiti a ƙasar waje bayan ta musanta rahotonnin da ke cewa ya rasu, tana mai cewa Manjo Janar Abdulsalami Ibrahim ne ya maye gurbinsa a matakin riƙon ƙwarya.
Daga baya hedikwatar tsaro ta Najeriya ta musanta batun, inda ta ce “babu wani batun muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa” a tsarin aikinta.