
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nemi gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya nemo masa filin da zai gina gidan da zai yi ritaya a jihar Anambra.
Shugaban ya bayyana hakane a yayin ziyarar sa ta farko a matsayin shugaban kasa a jihar ta Anambra inda ya kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar ta yi daban-daban.
Ya jinjinawa Gwamnan kan kokarin gyaran jihar da yake yi inda yace masa shima ya zama dan jihar Anambra a sama masa fili ya gina gidan da zai yi ritaya.
Shugaban dai ya fadi hakanne cikin raha.