
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya rantsar da gwamnan rikon kwarya na jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Étè Ibas (retd.).
Bikin rantsarwar ya samu halartar shugaban ma’aikata, Femi Gbajabiamila, da babban lauyan Gwamnati, Mr Lateef Fagbemi, SAN, da kuma sakataren shugaban kasa, Mr Hakeem Muri-Okunola.
Da misalin karfe 12:48 pm ne Ibas ya shiga fadar Shugaban kasar.