
Shuagaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nada AVM Sadiq Ismail Kaita a matsayin sabon shugaban kwamitin gudanarwa na jami’ar Bayero dake Kano.
Kaita ya maye Dr. Nasiru Yusuf Gawunane a wannan mukami.
Gawuna kuma shine shugaban hukumar kula da gidaje ta kasa.
A sanarwar da kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar Yace an cire gawuna daga shugabancin kwamitin gudanarwa na BUK ne dan ya mayar da hankali kan shugabancin hukumar kula da gidaje ta kasa
Gawuna dai na hannun damar tsohon shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne.