Tuesday, November 18
Shadow

Kungiyar kare hakkin musulmai ta Najeriya, MURIC ta nemi Gwamnati ta gina kotunan shari’ar Musulunci a kowace jiha

Kungiyar dake ikirarin kare hakkin Musulmai a Najeriya, MURIC ta bukaci Gwamnatin tarayya ta gina Kotunan shari’ar Musulunci a kowace jiha dake kasarnan.

Kungiyar tace dokar da ake amfani da ita babu adalci a ciki kuma akwai wasu sassa na kasarnan da babu kotunan Shari’a shiyasa take gabatar da wannan bukata.

Kungiyar tace dan hakane take bukatar gwamnatin tarayya kamar yanda aka gina manyan kotunan gwamnatin tarayya a kowace jiha to itama kotun shari’ar Musulunci a ginata a kowace jihar.

Shugaban kungiyar, Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Karanta Wannan  An min tayin Naira Miliyan 21 da takardar zama dan kasar Rasha, da fili dan in je in yiwa kasar yaki amma na kiya>>Sojan Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *