Thursday, January 15
Shadow

Shugaba Tinubu ya yi Allawadai ta juyin mulkin Guinea-Bissau

Gwamnatin Najeriya ta yi Allah Wadai da juyin Mulkin da aka yi a Guinea-Bissau, inda ta buƙaci a dawo da mulkin dimokraɗiyya a ƙasar.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar kula da harkokin ƙasashen waje na ƙasar ta fitar a yau alhamis, Najeriya ta ce ta damu matuƙa game da lamarin, inda ta bayyana ƙwace mulkin a matsayin ‘abin takaici’

” Juyin mulkin na bayyana karya dokokin ECOWAS na mulkin dimokraɗiyya da gwamnati mai adalci, waɗanda suka haramta hawa mulki ta hanyar da ba na tsarin mulki ba.” inji sanarwar.

Ma’aikatar harkokin wajen ta kuma ce Najeriya na tare da ƴan ƙasar Guinea Bissau, kuma ta na kiran dawo wa mulkin dimokradiyyar, da dawo da dukkanin waɗanda ake riƙe da su.

Karanta Wannan  Kalli Yanda wani matashi ya hau Saman karfen Sabis yace ba zai sauko ba sai Atiku Abubakar ya biyashi bashin Naira Miliyan 15 da yake binsa ko kuma ya kàshè kansa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *