
Shugaba Tinubu yace ya matsawa yan Najeriya ne saboda komai ya daidaita, kuma talaka zai sha jar miya nan bada dadewa ba.
Shugaba Tinubu yace tsare-tsaren sa na cire tallafin man fetur da sauransu da suka sa mutane cikin halin dauwa, nan gaba a’a ga amfaninsu.
Shugaban yace tuni an fara ganin Amfanin wadannan tsare-tsaren saboda farashin kayan Masarufi sun fara sauka.
Tun bayan da shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur ne dai aka shiga tsadar rayuwa a Najeriya wadda har yanzu ba’a dawo daidai ba.