Monday, December 16
Shadow

Shugaba Tinubu yace yana sane da halin matsin da ‘yan Najeriya ke ciki inda ya bayyana matakan kawo sauki da zai dauka

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sake jaddada cewa yana sane da halin matsin rayuwa da ‘yan ƙasar ke fama da shi.

Yayin da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamar da aikin titin Guzape Lot II, a Abuja babban birnin ƙasar ranar Asabar, shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya dace domin sauƙaƙa wa ‘yan ƙasar halin matsin rayuwar da suke fuskanta.

“Wannan lokaci ne mawuyaci a ƙasarmu,Har yanzu muna ƙoƙarin saisaita tsarin tattalin arzikin ƙasar, domin kawo sauƙi da ingantuwar tattalin arzikin ƙasarmu,” in ji Shugaba Tinubu.

Shugaban ƙasar ya ce kammala aikin titin alama ce ta abin da za a iya yi, ta hanyar abin da ya kira ”kyakkyawan tsari da haɗin kai da kuma aiki tare”.

Karanta Wannan  Domin Kawo Saukin Hauhawar farashin kayan masarufi, Gwamnati zata cire harajin VAT akan kayan abinci da ake shigowa dasu Najeriya

Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa ministan Abuja, Nyesom Wike, kan ƙoƙari da jajircewar da ya nuna wajen ayyukan waɗanda ke cikin alƙawuran da gwamnatin tarayya ta yi wa mazauna birnin Abuja.

”Haƙiƙa na yaba maka kan wannan jajircewa da ƙoƙarin da kake yi wajen kammala ayyuka”, in Shugaban

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *