
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai gana da kwamandojin tsaro da babban me bashi shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu dan shawo kan matsalar yawaitar kashe-kashen da ake samu.
Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya a daren jiya bayan kwashe sama da sati biyu yana hutu a Turai.
A yayin da yake wannan hutun an kashe mutane sama da 120 sannan an jikkata wasu yayin da aka raba wasu da muhallansu.
Jihohin da suka fi fuskantar wannan matsala sune Benue, da Filato.
Wata majiya ta bayar da tabbacin cewa, shugaban zai gana da masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro dan kawo karshen matsalar.