Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai halarci taro kan ci gaban kasashe a Abu Dhabi.
Taron zai wakanane ranar 12 zuwa 18 ga watan Janairu inda shi kuma shugaba Tinubu zai bar Najeriya ranar Asabar, 11 ga watan Janairun, kamar yanda me magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya sanar.
Onanuga yace Shugaban kasar UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne ya gayyaci shugaba Tinubu zuwa taron.