
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai gana da ‘yan kwallon kwado mata na Najeriya da ake kira da D’Tigress bayan da suka yi nasarar lashe kofin gasar kwallon kwando ta mata na Nahiyar Afrika.
Kamar dai yanda yawa ‘yan kwallon kafa mata, Super Falcons, shugaban ya sha alwashin tarbar ‘yan kwallon kwando mata, D’Tigress da kofin da suka ciwo.
A jiya, Lahadi ne dai D’Tigress suka lashe kofin bayan doke kasar Mali da ci 78-64 a wasan da suka buga a Abidjan, Côte d’Ivoire.
A sanarwar da me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar a madadin shugaban kasar, yace shugaba Tinubu ya yabawa ‘yan kwallon mata.
Shugaban, ya kuma jinjinawa me horas da ‘yan kwallon mata watau, Coach Rena Wakama.
Sannan yace kamar yanda ya karbi ‘yan mata masu kwallon kafa, Super Falcons, yana shirin tarbarsu suma a Abuja.