
Shugabancin jam’iyyar ADC ya musanta rahoton dake cewa, suna goyon bayan Atiku Abubakar ya tsaya takara shugaban kasa Peter Obi ya masa mataimaki
Shugaban jam’iyyar, David Mark ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata.
Ya bayyana cewa, Bashi da ikon zabar wanda zai zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
Yace jam’iyyar ta ‘yan jam’iyyar ce kuma ta ‘yan Najeriya ne.
Yayi kira ga ‘yan Najeriya da su shiga jam’iyyar ta ADC dan ganin an gyara Najeriya domin idan ba’a gyara ta ba, da kowa jirgin zai nutse.