
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, zai Rabawa mutanen kasarsa dala $2000 kowanne daga kudin Harajin da ya tara daga hannun kasashen Duniya.
Ya bayyana hakane a shafinsa na Truth social inda yace kasarsa ce kasa da aka fi girmamawa a tsakanin kasashen Duniya
Sannan ya yi alkawarin yin amfani da kudin Harajin wajan biyan bashin da ake bin kasar Amurka.
Saidai da yawa ‘yan kasar ta Amurka na shakka akan wannan ikirari nasa.